Babban Editan Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustaphan Sakkwato ya tattauna da masanin addinin Islama Imam Tukur Adam Abdullahi al-Mannar na Kaduna, a kan yawaitar filayen sallar Idi a wannan zamani da muke ciki.
Hakan na da nasaba ne da bambancin akida ko na ra'ayi, ko kuma da karuwar yawan jama'ar Musulmi?
Imam Tukur Adam Abdullahi al-Mannar yayi kira ga al'ummar Musulmi da a karfafawa mata guiwa su rika zuwa sallar Idi kamar yadda Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wa sallam ya koyar.