Shugaban hukumar ya bayyana halin da maniyattan Najeriya su 66,000 ke ciki yayin da ake gaf da hawan arafa gobe Laraba.
Yace alhazan Najeriya na cikin shiri da damarar fita domin zaman Minna da kuma zuwa hawan arafa. Hukumar alhazai ta kasa da hukumomin jihohi da malamai da suke aikin hajji sun tattauna kan hanyoyin da za'a bi a ci nasara a fitar Minna da hawan arafa da kuma zaman da za'a yi na jifan jamra.
Yace taron da aka yi a karkashin jagorancin mai martaba sarkin Kano ya cimma matsaya akan cewa hakika bai sabawa shari'a ba alhazan Najeriya su fara fita daren bakwai ga wata har zuwa takwas.
An inganta tantunan da alhazan zasu yi anfani dasu da kara wuraren kewayawa daga wurin tsuguno zuwa na boli da yin alwala da wanke hannu. Haka kuma sabbin shimfida aka sa a wuraren. Amma naura mai bada sanyi ta gaza saboda haka alhazan zasu ji zafi. Dole alhazai su shirya su fuskanci zafin.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5