Amma alhamdulillahi zamu ce wannan abu bai shafe su ba ta bangare rasuwa ba sai dai an samudan kalilan na mutum ukku zuwa hudu da suka samu raunuka wadanda kuma raunukan ba wadanda suke barazana bane ga ainihi rayuwar su.
Mutanen da kace sun samu raunukan an basu gado ne ko kuwa sun tafi sun ci gaba da harkokin su?
‘’A’a kamar yadda nayi bayani ai ba wani abu bane, irin dai dan buguwa ne haka, abubuwa ne ba masu tada hankali ba, wasun ma an basu magani an sallame su, akwai wadanda ma suka dimauta suka gigita kwarai da gaske, kuma hukumar Saudiyya duk ta kula da irin wadannan Alhazzai kuma an basu tallafin da ya kamata kuma an salami kowa ya tafi gida cikin namu mutanen’’
Ambasada kunbi dukkan masaukin alhazzan Najeriya kuka tabbatar kowanne na cikin koshin lafiya ko ko ta wane hanya kuka gane cewa ba wani dan Najeriya da wannan abu ya rutsa dashi?
‘’Dama duk lokacin da alhaji yazo nan ko a makka ko Madina ko ina ma yake , a ko wane lokaci akwai ido akan sa tunda anan mutum ba a gida yake ba, don haka wajibi a kowane lokaci cikin awa 24 akwai jamiai da ke tare dashi akwai na jihohi akwai na hukumar Alhazai, akwai jamian ofishin jakadanci da ako wane lokaci suke aiki suke sa ido akan halin da alhaji yake ciki’’
Ga Mamud Lalo da ci gaban Hirar