Gwamnatin Najeriya ta amince da ba likitocin kiwon lafiya da na hakori, cibiyoyin jinya, da kuma dakunan shan magani na gwamnatin Tarayya alawus din N25,000 kowanne wata biyo bayan yajin aikin da kungiyar NARD ta shiga.
Hakan ya fito ne a wata wasika mai kwanan wata 26 ga watan yuli, 2023, dauke da sa hannun Shugaban hukamar tara kudaden shiga da albashi ta Najeria (NISWC), Mr. Ekpo Nta, wanda ya bayyana cewa, za a kuma rika biyan alawus din daga kudaden gudanarwa na ma’aikatun.
A zantarwarsu da sashen Hausa na Muryar Amurka, Mataimakin Sakataren Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa NARD, Dr Nura Umar, yace, alawus din akwai ya babu ne, domin kungiyar tasu ta nemi ayi musu karin kaso dari biyu na albashin su ne.
Sakataren Kungiyar ya kara da cewa basu amince da karin kashi ashirin da biyar na albashin su ba, duba da yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa, suna bukatar albashi su ya koma darajar shi ta da shekara 9 baya.
Dr. Nura ya ci gaba da cewa, wannan baya cikin dalilansu na shiga yajin aiki. Yace akwai bukatun su guda biyu da suke ganin gwamnati zata iya aiwatarwa a kwana guda, da zai sa su janye yajin aikin da suke ciki, duk da cewa basu fayyace bukatun ba.
Daga karshe, Dr. Nura Umar yayi kira da gwamnati da ta duba halin da ma’aikatan lafiya da talakawan kasa suke ciki, tayi abunda ya kamata.
Saurari hirar Dr Nura da Hauwa Umar:
Your browser doesn’t support HTML5