Ala'kar Mata da Wayoyi Masu Tsada

Mata da Waya

A fannin mu na mata yau Dandali, ya waiwayi alakar mata, da manyan wayoyi, klam,ar yadda wakiliyar Dandali, Baraka Bashir, ta jiyo mana ra’ayoyin wasu mata.

“Gaskiya ina so in rike babban Waya saboda gaskiya yanzu ita ake yayi masamman fararen nan manya, ina jin dadi ni basan iya zama ma ba Waya ba.”

Shin Wayar da kike rikewa babba ce?

Yanzu dai ‘yar karama ce amma buri na dana samu kudi in canja katuwan nan.

Toh idan kika rike babbar Waya yaya kike ji a cikin sa’anin ki?

Ai wallahi jinka za kayi Kan ka ma dauka yake yi, gaskiya idan ka rike karamar Waya baka son fito da ita saboda kawaye suna da manya kai kuwa taka karama, boyeta kake yi a jaka wani lokaci idan an kira kana ji tana kararrawa zakayi banza da ita.

Amma wasu mutane idan sun je kamar unguwa in sun ga mutane sun fito da manyan wayar su wadanda keda kanana kunya zasu ji wajen fito da nasu, shi yasa yawanchi mata yanzu ke son wayayoyi masu tsada.

Kina nufin iya girman waya iya ajin Budurwa?

Wasu iya girman Wayar shine iya ajin su dan wasu akan waya ma sai a hankali, abun duniya dai sun ka sa a gaba.

Toh, ke a naki ra’ayin babbar Waya kike da burin ki rike ?

Kowane irin waya zan iya amfani dashi.

Ita kuwa wannan matar cewa tayi, “Gaskiya na damu sai na rike “Smart Phone” babbar Waya saboda yanzu shi ake yayi kuma da shine zaka samu kayi abubuwa kake bukata. Idan har ban rike babban Waya ba gaskiya jin nake yi kamar nima ban kai ba.