Babu shakka matakin rufe iyakokin Najeriya wani abu ne da har yanzu ke ci gaba da haifar da gunaguni a cikin al’umma sanadiyar koma bayan da matakin ya haddasa a fannoni da dama. Malam Nouhou Souley Dan Maradi, dake harkoki a tsakanin Nijer da Najeriya na daga cikin masu korafi akan wannan batu. Ya ce talakawan Najeriya na ci gaba da korafi haka kuma ‘yan kasuwa makwabtan Najeriya.
Tun a washegarin daukar wannan mataki hukumomin Najeriya suka bayyana cewa yawaitar aiyukan ta’addanci da satar shanu da garkuwa da mutane don neman kudin fansa ne ke mafarin tsaurara matakan zuba ido akan iyakar kasar da makwabtanta.
Boukary Sani Zilly, dan majalisar dokokin kasashen Ecowas ne ya ce, wannan yanayin da ake ciki a yanzu a fannin tsaro, ya yi tsananin da za a kara jan damara. Sai dai duk da haka dan majalisar ya ce zasu bi hanyoyin ankarar da hukumomin Najeriya game da abubuwan da dokokin Ecowas suka tsara akan maganar kai da kawon al’ummomi da dukiyoyinsu.
Ya zuwa yanzu dai jakadan Najeriya a Nijer bai maida martani akan wadannan korafe-korafen ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5