Kasancewa akwai dadaddar dangantaka mai karfi tsakanin Niger da Najeriya, wasu ‘yan jamhuriyar Nijer sun tofa albarkacin bakinsu game da sauke Sarki Muhammadu Sanusi na biyu da gwamnatin jihar Kano ta yi.
Alhaji Umaru Dangote mazaunin jihar Damagaram, ya ce a fannin masarauta abin da ya kamata a yi shi ne idan aka sauke sarki daga gidan Sanusi aka ba dan gidan Ado, dan gidan Ado ya ce ba zai karba ba, ko da yake abun bai zo da mamaki ba saboda akwai lakabin da ake yi masu mai cewa “ko da tsiya ko da tsiya-tsiya sai sun karbi Mulki.” Umaru ya kuma ce gwamnati ce ta kara assasa lamarin har ya kai inda ya kai.
A nasa ra’ayin, Isuhu Ibono cewa ya yi abin da ya faru kaddara ce daga Allah ko da yake wasu na ganin siyasa ta shiga lamarin. Isuhu ya kuma yi wa Najeriya fatan zaman lafiya.
Shi kuwa Darda’u Abdulrahaman, mazaunin jihar Damagaram, ya yi kira ne ga sarakunan gargaji da su fita harkokin siyasa saboda su iyayen jama’a ne gaba daya.
Ga Karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum