SOKOTO, NIGERIA - 'Yan gudun hijira da ke jihar Sakkwato, arewa maso yammacin Najeriya, wadanda ke zaune a wasu al'ummomi dake garin Tabanni a yankin Ghandi ta Rabah da harin ‘yan bindiga ya tarwatsa fiye da shekara 4 da suka gabata, sun yi dace da samun taimako daga kungiyar ayukkan agaji ta Qatar ta hannun hukumar zakka da wakafi, wadda ta gina musu gidaje na zamani har 150, da masallatai da assibiti da rijiyojin burtsatse da dai sauran abubuwan bukatar zaman al'umma ga wuri.
A hirar shi da Muryar Amurka, daraktan cibiyar ta Qatar Sheikh Hamdi Abdu ya ce sun yi wannan aikin domin ya amfani jama'a.
Yana mai cewa, “Da yardar Allah duk mutanen wurin zasu amfana da ilimi da lafiya da duk fannonin da cibiyar ta agaza, Alhamdulillah kowa ya ga yadda irin amfanin da muka samar na taimakawa jama'a, kuma muna bukatar gwamnatin jiha ta shirya wa yara dubu daya karatu mu dauki nauyin karatun su"
Gwamnatin Sakkwato dai ita ce ta baiwa cibiyar filin da ta gudanar da wannan aikin na taimako ga wadanda ibtila'i ya shafa, a cewar mataimakin gwamna Manir Muhammad Dan'iya.
Wannan cibiyar ta jima tana gunadar da ayukkan jinkai a Najeriya da kasashen duniya daban-daban.
Wasu masana da Muryar Amurka ta yi hira da su sun kalubalanci ‘yan Najeriya dake zaune tare da ‘yan gudun hijirar su yi koyi da wannan karamcin domin kawar da damuwa da halin kunci da wadansu 'yan gudun hijiran kan shiga.
Yanzu haka akwai dubban ‘yan gudun hijira wadanda tashe-tashen hankula suka raba da gidajensu a sassa daban daban na arewacin Najeriya wadanda akasarin su su ke cikin halin damuwa kamar wadansu da ke zaune a wani kangon gida da Muryar Amurka ta yi hira da su.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5