NIGER, NIGERIA - Al’ummar garin na Salka dake yankin karamar hukumar Magama a Jihar Nejan Najeriya, sun nuna damuwa ne akan yadda suka ce sarkin garin baya daukar matakin zaman Lafiya a tsakanin al’ummar da ya ke shugabanta.
Tun a kwanakin baya anyi wani tashin hankalin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutun biyar tare da kona kimanin gidaje 50, wanda a ciki har da ofishin ‘yan sanda da kuma gidan basaraken garin, al’amarin da ya sa sarkin garin ya yi gudun hijira.
A wani taron manema labarai da al’ummar garin Salkan suka gudanar a Minna, sun yi kira ga sarkin Sudan na Kontagora da ya hanzarta daukar mataki na dakatar da wannan Dagaci dake karkashin Masarautarshi.
Shugaban wata kungiyar matasa a garin na Salka, Malam Shu’aibu Alkali ya ce tun da Sarkin na Salka ya na zaman gudun hijira, to suna bukatar ya ci gaba da zama a can.
Alhaji Abubakar Abara shine Sarkin na Salka wanda ake korafi akan shi ya baiwa al’ummar da yake shugabanta hakuri.
To ita ma dai masarautar Kontagora ta ce tana sane da wannan dambarwa dake tsakanin mutanen wannan gari da sarkin na su, kuma suna daukar matakin shawo kan lamarin.
A halin yanzu dai Jama’a na cike da fatan ganin an shawo kan wannan zaman tankiya a tsakinin wannam Sarki da jama’arsa a wannan yanki da ke fama da matsalar ‘yan bindiga.
Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5