Al'ummar Kenya Na Jiran Sakamakon Zaben Shugaban Kasa 

Al'ummar Kenya na jiran sakamakon zaben shugaban kasa

Al'ummar Kenya dai na dakon sakamakon zaben shugaban kasar da aka kammala cikin kwanciyar hankali, inda jama'ar kasar suka kada kuri'a kamar yadda aka saba.

WASHINGTON, D.C - Zaben na ranar Talata ya kasance gwajin karshe da madugun 'yan adawa Raila Odinga ya yi, wanda a yunkurinsa na biyar ya samu goyon bayan tsohon abokin hamayyarsa kuma shugaba mai barin gado Uhuru Kenyatta.

Al'ummar Kenya na jiran sakamakon zaben shugaban kasa

Daya daga cikin wadanda ke fafatawa a zaben shi ne mataimakin shugaban kasar William Ruto, wanda ya yi kaca-kaca da shugaban a farkon shekaru goma da suka yi yana mulki.

Masu kada kuri'a sun bayyana damuwa ga rashin samun sauyi na hakika da kuma takaicin hauhawar farashin kayayyaki da cin hanci da rashawa a cibiyar tattalin arzikin gabashin Afirka.

Al'ummar Kenya na jiran sakamakon zaben shugaban kasa

Dukkanin manyan ‘yan takarar dai an dade da sanin su a kasar Kenya, Odinga a matsayin mai fafutukar neman dimokuradiyya kuma tsohon dan siyasa da kuma Ruto a matsayin hamshakin attajirin nan wanda ke nuna matashin kashin kansa sabanin daular da ta haifar da Odinga da Kenyatta.

Al'ummar Kenya na jiran sakamakon zaben shugaban kasa

Goyon bayan da shugaban kasar ke yi wa Odinga ya katse kabilun da aka saba da su da suka dade suna fayyace zabuka da kuma haifar da tashin hankali. A wannan karon babu wani dan takara daga babbar kabila ta Kenya, wato Kikuyu, ko da yake manyan 'yan takarar biyu sun zabi abokan takarar Kikuyu.

Dole ne a sanar da sakamakon zaben a hukumance a cikin mako guda na kada kuri'a, amma akwai hasashen wanda zai yi nasara a ranar Laraba.

-AP