Al'ummar IGDLAN Sun Bukaci Hukumomin Nijar Su Saka Harshensu Cikin Na Kasa

IGDLAN Njiar

A jamhuriyar Nijar al’ummar Igdalan dake zaune a yankin Tahoua da Agadez ta bukaci hukumomi su saka harshen Tagdal a sahun harsunan kasar ta yadda zasu fara morar dukkan wasu abubuwan da kasa ta yi tanadi domin ‘ya yanta, musaman abin da ya shafi tsarin karantar da yara a cikin harshen uwa.

A lokacin taron da suka gudanar jiya Lahdi a birnin Yamai, don tattauna batun shigar da harshen Taglan a jerin harsunan kasar Nijar, shugabannin al’ummar Igdalan sun jaddada wannan bukata da suka shafe shekaru suna fafutuka a kanta. Shugaban kungiyar ORDH Waila Iglas, na ganin lokacin ya yi da wannan al’umma za ta fara morar ‘yan cin da doka tayi tanadi domin ‘yan kasa.

Igdalan na daga cikin al’ummomin da suka kafa garin Agadez, inji masanan tarihi saboda haka sarkin Air mai martaba Sultan Ibrahim Oumarou ke cewa amincewa harshen Tagdal a matsayin harshe na 11 a wannan kasa abu ne da ya kamata a yi na’am da shi.

Da yake jawabi a lokacin bukin bude wannan taro ministan cikin gida Bazoum Mohamed ya bayyana cewa yana tare da su akan haka, kuma zai basu goyon baya a wannan gwagwarmaya domin mataki ne da ya yi dai dai da tanade tanaden kundin tsarin mulkin kasa.

Amincewar harshen Taglan a matsayin daya daga cikin harsunan Nijar, wata hanya ce da za ta baiwa yaran al’umma Igdalan damar samun ilimi a karkashin tsarin karantarwa cikin harsunan uwa wanda gwamnatin kasar Nijar ta soma zartar da shi.

A karshen wannan taron na wuni 1 mahalartan da suka hada da masanan tarihi, da sarakunan gargajiya, da dattawan al’ummar Igdalan, na da alhakin gabatarwa hukumomi shawarwarin da suka tsayar kafin daga baya a shigar da bukatunsu a zauren majalisar dokoki domin nazari akai.

Ga cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Al'ummar IGDLAN Sun Bukaci Hukumomin Nijar Su Saka Harshensu Cikin Na Kasa