Jama'a suna kira ga mahukunta da su dauki matakai, domin su dauki matakan aikin tsaro, sannan jama'a su lura wa kaiwa da kawowa.
Ganin cewa, iyakar tana da yawa tsakanin Birni N'Konni da Najeriya, kuma ga wannan labarin harin, shi ya sa lokacin da Ministan cikin gida, Bazum Mohamedda ya ziyarci Birni N'Konni a kan maganar tsaro, yace gwamnatin Nijar a shirye take domin daukar matakan tsaro a wannan yankin, ganin cewa akwai mutane masu aikata ayukan tashin hankali a wannan yankin.
Sai dai Alhadji Maman Dan Yaro yace, yana da kyau hukuma ta rinka bada kariya ga masu nema mata labarai.
Wannan iyakar ta jahar Tahoua da jahar Sokoto ta janyo tarurruka da dama a can baya game da wannan matsalar ta tsaro, domin toshe dukkan wata kafa, wanda mahara zasu iya arcewa.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Harouna Mamane Bako.
Your browser doesn’t support HTML5