Ita ma Al’ummar arewacin Najeriya mazauna Ghana ba a bar ta a baya ba, inda ta yi kira ga al’ummar Ghana da su bi dokara zabe, a gudanar da zaben bana lafiya ba tare da tashin hankali ba.
Sardauna Ahmadu Bello na Najeriya ne ya assasa kafa kungiyar al’ummar arewa a Ghana (Arewa Community-Ghana) shekaru 63 da suka wuce domin hada kai da zumunci da taimakawa duk al’ummar arewacin Najeriya dake zaune a Ghana, in ji Alhaji Ali Mohammed Shamaki. Ya ce, Sardauna ya ce da su idan sun kafa kungiya, ‘Haduwarsu wuri daya shi ne mafi muhimmanci, fiye da rabuwarsu, domin in sun hada hada kai, shi ne zai sa gwamnati ta san da zamansu, idan akwai abin taimakawa sai ta taimaka musu’.
Wasu shugabannin kungiyar sun yi fatan a gudanar da zaben Ghana lami lafiya, sanna kuma suka yi kira ga jama’a da su kiyaye daga duk abinda zai kawo fitina. Kamar yadda Malam Musa Maihula, jami’in shirye-shirye na kungiyar yace, ‘Duk duniya maganar Ghana ce a kan gaba, domin haka matasa; maza da mata da ‘yan siyasa ya kasance kasa suka sa a gaba, ba burin kansu ba’.
Wasu ‘yan kungiyar sun yi fatan alheri tare da addu’ar cewa Allah Ya sa a yi zabe lafiya, tare da zaben wanda ya fi alheri gag a Ghana.
Za a bude rumfunan zabe na masu kada kuri'a miliyan 18.7 da suka yi rajista da karfe 7:00 na safe, ranar Asabar 7 ga watan Disamba, kuma a rufe a karfe 5:00 yamma.
Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdullah:
Your browser doesn’t support HTML5