Kungiyar ci gaban al'ummar Adara a jihar Kaduna ta koka a kan ganin wani jirgin sama a lokacin da 'yan bindiga su ka kai hari kan garuruwan Dogon noma da Unguwar Sarki da ke karamar hukumar Kajurun a jihar, inda aka kashe mutane 32 Ranar Alhamis. Sai dai gwamnatin jihar Kaduna ta ce jirgin sojan sama ne ya je kai wa al'ummar dauki, ba na 'yan bindiga ba.
Wannan bayani da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan ya yi, bai sauya tunanin kungiyar ci gaban al'ummar Adara ba saboda shugaban kungiyar, Mr. Awemi Dio Maisamari, ya ce akwai wasu alamun tambayoyi game da zuwan jirgin.
Maisamari ya ce tun daga shekarar 2013 masu satar shanu suka fara kai musu hari har aka zo ga satar jama’a don neman kudin fansa. Sai kuma gashi a kwanan nan mazauna yankunan sun shaida ganin wani farin jirgin sama a daidai lokacin da aka kai musu hari kuma babu wanda ya kai musu dauki.
Gwamnatin jihar Kaduna dai ba ta kara cewa komai ba game da zargin ba, ko da ya ke sanarwar da kwamishinan tsaron jihar ya fara fitarwa ta tabbatar da cewa jirgin sojan sama ne ya kai wa al'ummar Dogon noma dauki.
Masani kan harkokin tsaro Dakta Yahuza Ahmed Getso, ya ce an ga irin wannan lamarin a jihar Zamfara, Katsina, Neja, da Sokoto inda jirage ke zuwa su sauke makamai da kai kariya, amma idan gaskiya ne sojoji ne suka kai dauki a yankunan na jihar Kaduna me ya sa ba su kare jama’ar ba har sai da aka kashe mutane da yawa?
Shugaban kungiyar al'ummar Adara Mr. Maisamari ya kara da cewa koma dai me ya faru, al’ummar yankunan guda biyu da aka kashe musu mutane sama 30 aka kuma kone musu dukiya suna bukatar taimako daga gwamnati.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5