Akalla mutane 16 aka kashe wadanda yawancin su sojojin gwamnati ne, biyo bayan harin da 'yan ta’addan Al-shabab suka kai a wani karamin gari mai suna Beled Hawodakecikin da ke kasar Somalia,
A jiya Litinin wannan hari ya faru, kamar yadda jami’ai da kuma mazauna inda abin ya faru suke cewa.
Harin na farko an auna barikin soja ne wanda yake da tazarar kilomita 6 daga wajen garin na Beled Hawo.
Magajin garin, Mohammed Hayd ya shaidawa Sashen Somalia na Muryar Amurka cewa sai da 'yan ta'addan suka ta da bam da ke cikin wata mota kafin su dunfari sansanin sojojin.
Hari na ukkun kuwa maharan sun auna babban hedkwatar gundumar garin ne.
Sai dai yayin da mayakan na Al shabab da sojojin Somalia suke arangama, suma sojojin kasar Kenya sun kaddamar da harin dakile wa ‘yan Al-shabab din hanyoyin shiga cikin kasar ta Kenya.