Kungiyar kamfanonin dake buga Burodi a yankin arewacin Najeriya, sun yi barazanar tafiya yajin aiki idan ha ba a janye Karin farashin da aka yiwa fulawa a ‘yan kwanakin nan.
A yanzu dai dilolin dake sayarda fulawa a yankin arewacin Najeriya, sun mayarda farashin buhun fulawa akan Naira 14,500 a maimakon Naira dubu 9,000 zuwa 10,000 da ake sayarda shi a cikin makoni biyu da suka gabata al’amarin da masu buga burodin suka ce ya jefa su cikin mawuyancin hali.
Shugaban kamfanin “Shukura Bread” Alhaji Lawali Muhammad, kuma mataimakin shugaban kwamitin amintattu na kungiyar masu kamfanonin burodi a yankin arewacin Najeriya, yace ‘yan kungiyar sun yi duk hakurin da yakamata suyi amma tura tana neman ta kai bango ta inda sai sunyi Karin kudin burodi abinda basu son ya faru.
Ya kara da kira ga hukumomi dasu dubi wannan al’amari da idon basira domin a cewarsa idan har suka yi Karin farshin burodi, toh lallai talaka zai shiga wani hali na rashin tabbas akan wannan batun na Karin kudi.
Daya daga cikin dililin dake sayar da fulawa Alhaji Abubakar Magaru, yace tashin farashin kudin motar dake yi masu dakon daga Legas zuwa arewacin Najeriya, a sakamakon karyewar gadar Tatabu shine dalilin Karin farashin kudin fulawar a yankin arewacin Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5