Akwai Yiwuwar Samun Yanayi Mai Sarkakiya Da Ka Iya Kawo Cikas-Inji Salisu M Ofisa

Sakataren babbar hadaddiyar kungiyar masu shirya fina-finan Hausa, wato MOPPAN dake jihar Kano, Salisu Muhammad Ofisa, ya ce akwai yiwuwar samun wani yanayi mai sarkakiya da ka iya kawo cikas ga yarjejeniyar da suke niyyar kullawa da ‘yan downloading.

Ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA inda ya ce akwai yiwuwar wasu daga cikin ‘yan downloading din ba zasu sami damar sayar da fim dinsu ba, kuma ba zasu bi ka'idojin da aka gindaya masu ba domin da zarar wani babban dan downloading ya sami sayen wani fim, zai iya raba shi ga sauran ‘yan downloading ba tare da sun biya kudin saye ba, a cewarsa hakan nakasu ne ga yarjejeniyar da zasu kulla.

Salisu ya ce hakan zai iya dawo da harkar Kannywood gidan jiya duba da cewar shigo da ‘yan daownlaoding cikin harkar kasuwancin fina-finai bata da wani kariya ko wata doka illa idan suka saba ‘yarjejeniyar suna da hurumin kai su ga kotu.

Ofisa ya ce wasu zasu iya sayen kayan ‘yan fim su nuna, wasu kuwa zasu saya su kuma ki nunawa wanda hakan cuta ce da ka iya tauye manufar shigar da wannan sabon kudiri.

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Yiwuwar Samun Yanayi Mai Sarkakiya Da Ka Iya Kawo Cikas-Inji Salisu M Ofisa

Daga karshe ya bayyana cewa yin hakan kuwa na nuni da cewar satar fasaha na nan daram ba inda ta je muddin basu amince da yarjejeniyar ba cuta babu cutarwa, akasin hakan kuwa koma baya ne ga masana'antar.