Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Bana Ra'ayin Waka Sakamakon Yadda Malamai Ke Kushe Ta - Inji Sky Bizamanga


Babban buri na a matsayi na na mawaki shine in daga harshen Hausa a sassa daban-daban na duniya don harshen ya inganta kamar sauran harsuna kamar harshen Turanci da Larabci inji mawaki Umar M Lawal wanda aka fi sani da Sky bizamanga.

Umar ya ce ya kasance wanda baya ra’ayin waka a da, sakamakon yadda malamai ke kushe waka da sanya wa dalibai kin waka a zukatansu.

Ya kuma fara waka ne bayan da wata rana sun je wata makaranta gasa, aka kuma bukaci da su rubuta waka, ya rubuta ya kuma samu sa’a daga nan ne ya sauya ra’ayi har ya fara waka.

Ya ce da wakarsa ne yake jan hankalin matasa wajen kauracewa yaudara da rayuwar karya musamman ga ‘yan matansu ko tsakanin sha’aninsu na kai kansu inda Allah bai kai su ba.

Daga karshe ya ce, ya kamata matasa su jajirce wajen neman abin dogaro da kai, ya ce da farko ya fara ne da harkar fim wanda sanidayarsa ne ya tsunduma ga waka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:00 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG