Shugaban Amurka Donald Trump, jiya Litinin, ya ce, “akwai matukar yiwuwar ya gana da Shugaban Iran, Hassan Rouhani, cikin ‘yan makonni masu zuwa, don a sake tattaunawa kan wata sabuwar yarjajjeniya ta kawo karshen shirin nukiliyar Iran.
Sabuwar yarjajeniyar za ta maye gurbin ta kasa da kasa ta 2015, wacce Trump ya janye daga cikinta a bara.
Trump, wanda ke magana bayan taron G7 na shugabannin manyan kasashen duniya a Faransa, ya ce, “ina ganin Iran za ta zo ta bukaci a gana.”
Shugaban na Amurka ya ce takunkumin tattalin arzikin da ya sake kakaba wa Iran shekara guda da ta gabata ya na, a cewarsa, “addabarsu matuka,”ganin yadda shi Trump din ya yi matukar takaita hanyoyin sayar da man Iran a kasuwannin duniya.
Da ma shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya sha kokarin shirya tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran.
Macron ya gaya ma wani taron manema labarai a gaban Trump cewa ya tattauna da shugaba Rouhani kuma, inji shi, shugaban na Iran na da niyyar ganawa da Trump.