Akwai Yiwuwar Fuskantar Karancin Abinci A Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya

Kayan kwashe amfanin gona.

Baya ga rayuka, wani batu da rikicin Boko Haram ya shafa matuka shine harkar noma, sakamakon raba dubban manoma da gonaki da kuma gidaje, lamarin dake kara barazana ga harkar samar da abinci.

Kuma ko a cikin kwanakin nan masana na gargadin cewa akwai yuwar fuskantar karancin abinci musamman a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

To sai dai kuma yayin da hankula suka kwanta, aka koma wasu yankunan da aka kwato daga hannun mayakan Boko Haram, wani batu da al’ummomin da suka koma ke kokawa shine batun tallafin noma ga al’ummomin da suka koman.

Alal missali a jihar Adamawa daya daga cikin jihohin da rikicin Boko Haram ya tarwatsa akwai dubban manoman da rikicin ya raba da gonaki, yayin da aka samu wasu jama’a da yanzu ke tallafawa irin wadannan manoma.

A ziyarar da ya kai sansanin yan gudun hijira na malkohi, gwamnan jihar Adamawa, Sanata Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla, yace gwamnatin jihar ta tanadi wuraren noma ga yan gudun hijira tare da tallafa musu wajen samun tallafi daga gwamnatin tarayya.

Yankin Malkohi, yanki ne dake da sansanin yan gudun hijiran Boko Haram, baya kuma ga wadanda suka zama yan gari sakamakon karbarsu da jama’an garin suka yi da har suka basu matsuguni da kuma wuraren noma da kiwo.

Mallam Idrisa Abdullahi dake zama shugaban yan gudun hijiran da aka tsugunar ya yaba da irin taimakon da al’umman Malkohin suka basu.

Wannan ma ko na zuwa ne, ayayin da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa a Najeriya (NEMA) ke maida martani ga rahoton da ake fitar da ke nuni da cewa yara kusan 50,000 ka iya mutuwa saboda kamuwa da tsananin tamowa musamman a Arewa maso Gabashin kasar.

Hukumar ta mayar da martani ne ga babban jami'in Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) mai kula da samar da abinci mai gina jiki, Arjan de Wagt.

Babban jami'in hukumar NEMA mai kula da yankin na arewa maso gabashin Najeriya, Muhammad Kanar, ya karyata rahoton da cewa ba gaskiya.

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Yiwuwar Fuskantar Karancin Abinci A Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya - 3'57"