Akwai Sojojin Najeriya a Boko Haram - inji Sojan Najeriya - Kashi na Uku

Wani mutum da yace shi sojan Najariya ne daga Kwanduga a jihar Borno, ya fadi irin abubuwan dake wakana a bayan fage, dangane da yaki da kungiyar tayar da kayar baya da aka fi sani da Boko Haram, a hirar da yayi da Aliyu Mustaphan Sokoto na sashen Hausa. Ga kashi na uku na hirar.
Aliyu Mustaphan Sokoto: To, yanzu kai a taka fahimta mai yasa ake zuwa ake hadaku da juna, kuna kashe junanku.

Soja: Ni dai ina gaya maka wannan gwamnatin da muke ciki suna "business" ne na neman kudi, sai kuma suka koma suna amfani da rayukan mu saboda su cika burin su. Boko haram rana daya za’a iya gamawa dasu duk wanda yace ma za’a dauki kwana biyu ko uku karyane, rana daya Najeriyan Army zata iya gamawa da su in ta shirya, amma ni kam Najeriyan Army bata shirya ba kuma baza suyi amfani da ni ba. Raina yafi karfi, ina son raina fiye da, ni kadai ban isa in gama da "problem" na Najeriya ba, toh su cire kudin nan su kawo su biyamu ma hakkin mu na aikin da mukayi a nan tun January. Ina nan ban ci abinda ya kai dubu hamsin ba kafadawa duniya, ina fada, sunana ne kawai bazan kira ba, wanda ya san muryata yaji, amma yau tun January an hanani zuwa Sallah, an hanamu zuwa Christmas, wai muna Kwantagora muna "training", training din banza training din wofi, mun zo nan kuma da training a jikinmu a bari muyi aiki an ki, sai dai a turamu jiki banza, common life jacket ba’a bamu ba, common life jacket rigan karfen nan da ake sawa mai kare bullet munyi complaint an hana mu, wai ai yaran almajirai ne, to bari in gaya maka ba yaran almajirai bane. Wadannan trained soja’s ne daga kasashen ketare, da yaran Nijar, da Chadi da Libiya duk suna cikin su, kaga wannan yafi karfin almajiri ko.

Aliyu Mustaphan Sokoto: A cikin su 'yan boke haram akwai mutanen da ba 'yan Najeriya ba.

Soja: Akwai 'yan Libiya, akwai 'yan Nijar, akwai 'yan Chadi sannan kuma akwai sojojin Najeriya wadanda ake zuwa ayi hayansu zo suyi masu aiki su koma bakin aiki.

Aliyu Mustaphan Sokoto: Suna fada a gefen 'yan boko haram, suna fada da ku?

Soja: Kaga kamar da yanzu da ake kashe mu, sai labari yaci gaba za’a ce za’a kara turo miliyoyin Nairori wa GOC, saboda ya kara karfi da kayan aiki waye-waye bari in gayamaka, kudi yana aljuhunsa kuma MG (Machine Gun) din da yayi mana alkawari yabamu sabon kira mai dogon zango yaki yaba mu sai dai yabamu mai 'yan kananan magazine muke rikewa wanda in ka harbi mutum biyu, uku magana ta kare kafin ka koma isa armo ma armo ma babu.

Aliyu Mustaphan Sokoto: Akwai yanzu sojoji irinka.

Soja: Ranar Juma’a tun karfe taran dare har safe karfe shida wuta yana zuba akan mu, to bari in gayamaka, makamansu yafi wanda muke amfana da shi, bullet din su ma 'yar Kaduna ce wa yake basu, aje a gayawa duniya an daina zaluntar yaran sojojin da suke ta diba suna zuwa sun kashewa saboda suma suna da iyaye suna da iyali.

Aliyu Mustaphan Sokoto: Akwa sojoji da yawa irinka da suka...

Soja: Rana daya ne za’a yi ta, ta kare, wadanda aka ajiye su anan kusan shekaru biyar, dukkansu 'yan boko haram ne, dukkansu ka fadawa duniya na fada, inba 'yan boko haram ba, yaya za’a yi kana zaune, da "enemy" tsakanin ka dashi kilometer biyu har kayi shekara biyar bai kaimaka hari ba, kayi shekara biyar kana zaune lafiya in an ce ka kai masa hari, sai kayi tafiyar mita hamsin ko talatin sai ka yanko kwana kace ai baka iyaba har yau yana wuri, wai yana ce mana "is act of cowardice" jiya mun so mu ritsa shi bamu san ya gudu ba.

Yanzu kusan kwanaki biyar kennan Sashen Hausa yake neman hukumomin Najeriya, a ciki harda yawan kiran babban sakataren ma'aikatar tsaron Najeriya, Alhaji Aliyu Noma domin mu basu damar mayar da martani ga wadannan kalaman amma bamu samu ji daga wajensu ba.

Sannu ahankali, zamu kawo muku ragowar wannan hira a kwanaki masu zuwa.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojan Najeriya ya fasa kwai kashi na uku - 3'35"