Ma'aikatan Lafiya 400,000 Da Najeriya Take Da Su Sun Yi Kadan - Dr. Pate

Babban ministan lafiya na Najeriya, Dr. Muhammad Ali Pate

Babban Ministan Lafiya na Najeriya Dr. Muhammad Ali Pate ya ce akwai likitoci da sauran jami'an lafiya sama da 400,000 a Najeriya amma ba su wadatar ba don haka akwai bukatar kari.

Muhammad Pate ya nuna shirin shawo kan hankalin kwararrun likitocin Najeriya a ketare su rika waiwayowa don taimakawa lamurran jinya a cikin gida.

Ministan wanda yake magana a karo na farko bayan amsar madafun iko da ganawa da dukkan sassan ma'aikatar lafiyan, ya ce hakika akwai jami'an lafiya musamman a yankunan karkara da ke kula da masu jinya.

Ya kara da cewa, akwai bukatar a ba su kwarin gwiwar yin hidima ga kasa.

Taron shawo kan likitoci su daina tafiya yajin aiki

Dr. Pate ya nuna damuwa cewa kimanin kashi 90% ko fiye na magunguna da sauran kayan jinya da a ke amfani da su a Najeriya daga waje a ke shigo da su.

Ya kara da cewa Najeriya za ta samar da wani tsari da za a rika samar da su a cikin gida.

Minista Pate ya sha alwashin bin dukkan hanyoyin shawo kan likitoci su daina tafiya yajin aiki don tallafawa marasa galihu.

Taron shawo kan likitoci su daina tafiya yajin aiki

Ministan ya gudanar da zaman ganawa da manema labarai da karamin ministan lafiya Dr. Tunji Alausa.

Dr. Alausa a nasa jawabin ya maida hankalin ne kan amfani da adana bayanan majinyata a na'ura don saukaka ba da kulawa a ko'ina.

"Za mu maida hankali wajen tara bayanan majinyata don haka in ya shiga wannan asibiti a wannan gari to gobe in ya shiga asibitin a wani gari sai kawai a duba na'ura a ga bayanan don ci gaba da kulawa da shi"

Ficewar kwararrun likitoci daga Najeriya zuwa ketare don samun albashi mai kyau na daga cikin kalubalen kiwon lafiya a Najeriya.

Minista Pate ya ce akwai boyayyun kwararru a cikin gida da za a fito da su fili don mutane su rika amfana da kwarewarsu.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Ma'aikatan Lafiya 400,000 Da Najeriya Take Da Su Sun Yi Kadan - Dr. Pate