Moammar Gaddafi na da daddiyar alaka da Azbinawa da kuma makiyayan Niger, kasar da dakarun da ke biyayya ga Gaddafi su ka shiga da yammacin Litini.
Kanar Gaddafi ya taba goyon bayan wani boren kabilar Azbinawa a arewacin Niger, kuma daruruwan tsoffin dakarun tawayen sun taimaka masa a yakinsa da ‘yan tawayen Libiya.
Azbinawan dai na zama ne a gabashin Sahara, akasari a Niger da Mali. Azbinawa akasashen biyu sun yi ta bore cikin ‘yan shekarun nan don neman karin cin gashin kai.
Cikin shekaru 10 da su ka gabata, Kanar Gaddafi ya yi ta kokarin ganin Libiya ta kyautata dangantakar ta da sauran kasashen Afirka, ya kuma yi amfani da dukiyar man sa wajen inganta ma’amalarsa da shugabannin wannan nahiyar.
Wasu kasashen Afirka na cigaba da daukar Gaddafi a matsayin Shugaban Libiya. To sai dai Jamhuriyar Niger ta amince da Majalisar Shugabancin Wucin Gadin Libiya da ke adawa da Gaddafi a matsayin halastacciyar hukumar kasar.