Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Taron Birnin Paris Ya Tsara Yadda Za a Tallafawa Libiya


Shugaba Nicolas Sarkozy na kasar Faransa tare da Mustapha Abdel Jalil da kuma Mahmoud Jibril, shugabannin wucin gadin kasar Libiya a fadar shi ta Elysee jim kadan kafin babban taron Paris
Shugaba Nicolas Sarkozy na kasar Faransa tare da Mustapha Abdel Jalil da kuma Mahmoud Jibril, shugabannin wucin gadin kasar Libiya a fadar shi ta Elysee jim kadan kafin babban taron Paris

Manyan kasashen duniya masu halartar babban taro a Paris sun yiwa Libiya alkawarin dubban miliyoyin dololi

Manyan kasashen duniya da ke halartar wani babban taro a birnin Paris na tsarawa Libiya yadda za a gudanar da wasu ayyuka nan gaba a ciki har da alkawuran da su ka yi na sakin dubban miliyoyin dalolin kasar da aka dakatar don a taimakawa hukumomin wucin gadi.

Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya gayawa mahalarta taron cewa cibiyoyin yin ayyukan kyautatawa jama'ar kasar Libiya na cikin wani hali na rauni, a yayin da kuma ake ci gaba da fada jefi-jefi a wasu sassan kasar. Ya ce an fara shirye-shiryen tsara yadda za a aiwatar da ayyukan agajin jin kai da kyau kamar yadda ya kamata da kuma taimakawa 'yan kasar Libiya a kan lokaci.

Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton ta gayawa wakilan da ke halartar babban taron cewa ya kamata Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin sassautawa Libiya matakan tsaurin da ta dauka a kan ta. Haka kuma ta ce Amurka ta fitar da dola miliyan dari bakwai daga cikin dukiyar kasar Libiya dola miliyan dubu daya da rabin da aka sakar ma ta a makon jiya.

Kasashen Amurka da Holland da kuma Faransa sun yi alkawarin sakin kusan dola miliyan dubu biyar daga cikin kudaden da aka hana gwamnatin Moammar Ghadafi lokacin da ta ke yakar 'yan tawayen da ke neman ganin bayan mulkin shi na shekaru 42.

Haka kuma a yau alhamis, Tarayyar Turai ta yi sanarwar dage takunkumin da ta zargawa wasu kadarorin kasar Libiya ishirin da takwas da su ka hada da tashoshin jiragen ruwa da bankuna da kuma kamfanonin makamashi.

XS
SM
MD
LG