An sami rahotanni masu sabani kan gaskiyar an ga jerin gwanon motoci dauke da sojoji masu biyayya ga hambararren shugaban Libya Moammar Gadhafi, sun tsallaka sun shiga Niger.
A yammacin jiya talata, wasu manyan kusoshin gwamnati Nijar uku sun karyata cewa fiyeda motocin soja metan daga Libya sun shiga kasar, suka ce motoci uku ne suka shiga kasar.
Jaridar New York Times ta ambaci ministan shari’a Marou Amadou, yana cewa jerin gwanon motoci uku ne kacal, kuma basu da makamai. Shugaban rundunar tsaro na Gadhafi, Mansour Dhao ne da wasu mukarrabansa cikin motocin da a iya saninsa suka shiga kasar.
Kamfanin dillancin labarai na Asscociated Press, ya ji ta bakin babban jami’in harkokin mulki na shugaban Nijar yana cewa, Mansour Dhao da ya tsallaka ya shiga kasar, an rako shi daga kan iyaka zuwa birnin Niamey, kuma yana wani gida da jami’an tsaro suka sakawa ido sosai.
Babban jami’in mulkin, Massoudo Hassoumi, yace shaidu da suka bada labarin ganin jerin gwanon motoci masu yawa sunyi kuskure, domin motocin na gwamnatin Nijar ne data tura domin su raka ‘yan kasar Libyan. Ya kara da cewa “gungun” mutane da aka gani suna tsallakowa daga Libya, galibinsu mayakan abzunawa ne ‘yan kasar Nijar din da Mali da suka taya Gadhafi yaki a rikicin kasar.
Tund a farko, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bada labarin jerin gwanon motoci dake dauke da manyan kusoshin gwamnatin Moammar Gadhafi, ciki harda wasu kwamandoji sun doshi Niamey, babban birnin kasar. Wata kakakin ma’aikatar Victoria Nuland, tace Gadhafi baya cikinsu, wadda ya gaskanta bayanin da ministan harkokin Nijar ya bayar tun da farko kan wan nan batu.