Tsohon dattijo Ahmad Joda, ya ce Najeriya ba zata rabu ba, ganin irin gwagwarmayar da rikita-rikitan da aka sha a baya, daga yakin basasa har zuwa rikicin 12 ga watan Yuni, amma har yanzu kasar a dunkule take wuri guda.
To sai dai kuma, Ahmad Jodan wanda shi ya jagoranci kwamitin da shugaba Buhari ya kafa domin duba hanyoyin tada komadar kasa, na ganin akwai bukatar gyaran fuska a wasu fannonin, inda yayi kira da a kirkiro da gundumomin da jama’a zasu amfana maimakon mazabun majalisar dattawa da ake da su yanzu domin magance koke-koke da matsalolin da jama’a ke ciki.
Tun farko da yake yaye kallabin taron na jihohin Adamawa da Taraba, gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla, ya ce koda yake akwai bukatar samun gyara a wasu fannoni da kason da ake baiwa jihohi da kuma samun yan takara masu zaman kansu to amma al’ummar jihar basu goyi bayan duk wani yunkuri na raba kasar ba.
Batun sake fasalin kasar na ci gaba da janyo cece-kuce, inda wasu ke ganin bai dace ba, yayin da wasu kuma ke ganin dacewarsa.
Da yake bayyana ra’ayinsa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce akwai bukatar duba wasu batutuwa.
Kawo yanzu tuni har wasu yankuna suka dau matsaya, yayin da watanni uku kwamitin da APC ta kafa zai kwashe yana gudanar da aikin ji da kuma tattara ra’ayoyin jama’a kan wannan batu.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul'aziz.
Your browser doesn’t support HTML5