Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Taron Dinke Rarrabuwan Kawuna da Ya Addabi Najeriya


 Matasan Najeriya daga sassa daban daban
Matasan Najeriya daga sassa daban daban

A babban birnin tarayyar Najeriya , Abuja, an yi wani taro da ya tattaro masana, shugabanni, 'yan kasuwa, jami'an tsaro da dai sauransu domin lalubo bakin zaren dinke rarrabuwan kawunan 'yan Najeriya saboda kasar ta cigaba

Taron yayi kokarin gano bakin zaren banbance banbance da kowane bangaren kasar ke ikirari domin a zauna lafiya.

Farfasa Anya O. Anya daga jihar Abia shi ya fara shimfida a wajen tattaunawar. Yana mai cewa a duba banbance banbancen al'adunmu wadanda "idan aka yi la'akari dasu ka iya zama madaurinmu da zasu karfafa zamantakewarmu". Ya cigaba da cewa "idan an yi la'akari da yadda matasan kasar daga sassa daban daban ke yin tawaye dole ne dattawan kasar su tashi su shawo kansu domin a cigaba da zama kasa daya dunkulalla".

Tsohon ministan labarai Farfasa Jerry Gana yana ganin sai an sake fasalin kasar tukun. Yana mai cewa "a kowace kasa dake da banbancin addini, al'adu, harsuna, dabi'u da dai sauransu gwamnatin tarayya a keyi yadda akwai abubuwan da jihohi zasu yi kana akwai na jihohi". Yace "amma a shirin Najeriya komi ya taru a hannun gwamnatin tarayya ne. Komi za'a yi sai an tunkari Abuja. Bai kamata a yi haka ba. Ana mulki kaman na soja wanda lokacinsu komi na hannun gwamnatin tarayya. Idan ana son zaman lafiya, jihohi a basu isasshen aiki da zasu yiwa mutanensu. Idan an yi hakan mutane ba zasu damu da Abuja ba".

Shi kuwa Injiniya Buba Galadima yana ganin ana "yamutsa addini da siyasa da kuma son zuciya a harkokin kasar". Ya bada shawara yana cewa "babbar matsalar da ta shafi kowa ita ce katsalandan da shugabannin addinai su keyi kamar suna gasa da juna. Sun manta hanyoyin addini sun koma kan siyasa". Yace "Muddun bamu kawar da irin wadannnan daga cikin halayenmu ba Najeriya ba zata taba cigaba ba".

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG