A sanarwar ta jiya Laraba gwamnatin jihar Sokoto tace ta haramtawa kungiyar Shiya reshen jihar, ayyukanta saboda suna kokarin jawo tashin hankali a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa an dauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Tuni kungiyar ta Shiya tayi kakkausan suka akan dokar wadda tace ta tauye masu 'yancin gudanar da addininsu kamar yadda kundun tsarin kulkin kasar ya tanada wa kowa.
Malam Kasumu Umar Yuni Tawai shi ne shugaban mabiya darikar Shiya a jihar Sokoto yana mai cewa basu san wane dalili ya taso ba har a ce an dakatar da "'yanuwa daka gudanar da ayyukansu na addini" wanda gwamnatin jihar Sokoto tayi. Yace suna mamakin lamarin.
Dangane da ko gwamnatin ta dauki matakin ne domin gujewa tashin hankali, shugaban shiyar yace duk inda suka zagaya tare da jami'an tsaro suke su ne kuma zasu iya fada ko akwai tashin hankali. A cewarsa wadanda basa son "'yanuwa" ne suka zuga gwamnati daukan matakin.
Shugaban yace matakin da zasu dauka shi ne na fadawa duniya cewa an mayar da su saniyar ware tamkar su ba 'yan kasa ba ne. Abu na biyu zasu nuna an hanasu yin addinin da su suka sani duk da cewa kundun tsarin mulki ya ba kowa yin addininsa ba tare da tsangwama ba.
Haramta ayyukan 'yan Shiya ya biyo bayan taron tsaro ne da aka yi. Kakakin 'yansandan Sokoto DSP Ibrahim Abayas yana mai cewa gwamnati ba zata yadda da kungiyar dake yiwa zaman lafiyar jama'a barazana ba tare da dukiyoyinsu. Ba zata yadda kungiyar tana tada hankalin jama'a ba, tana kuma cin zarafin al'umma.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.
Facebook Forum