Wata kungiyar masu rajin kare hakkin bi’adam a Najeriya mai suna “SERAP” sun kaddamar da wani taro don kara jawo hankalin mahukunta, dangane da bukatu da ake da su wajen tallafama mutane da suka shiga cikin halin kakani kayi, a sanadiyar rikicin boko haram da ya’addabi yankin arewa maso gabshin kasar.
Suna ganin ya kamata gwamnatoci su taimaka wajen inganta rayuwar mutane, dake zaune a sansannin ‘yan-gudun hijira da suke a jihohin Adamawa, Gombe, Kaduna, Bauci, da birnin Tarayya Abuja, dama duk inda ‘yan-gudun hijirar suke. Kungiyar na ganin cewar mutanen nan na bukatar taimakon gaggawa, domin irin halin da suka samu kansu a ciki, hali ne da bai kamata ace mutun na ciki ba.
A dai tabakin babban darakta a kungiyar, Adetokunbo Mumini, yace babban dalilin da yasa suka kaddamar da wannan taron shine, don su bayyanar da halin da mutanen ke ciki, da kuma bayyanar da bukatun su, kana kada a kuma manta da su. Don haka akwai bukatar gwamnatoci da masu hannu da shuni su kokarta wajen inganta rayuwar mutane a kowane hali.
Ganaral Shola Williams, tsohon gwamnan mulkin soja a jihar Lagos, yayi karin bayani akan irin matakan da suka dace, ace gwamnatoci sun dauka wajen inganta rayuwar mutane, da ke gudun hijira a fadin kasar. Yana ganin cewar ya kamata abarma hukumar kula da ‘yan-gudun hijira su dinga daukar nauyin mutane, ba ace wata hukuma ba. Don yana ganin cewar hukumar agajin gaggawa ta “NEMA” ta dauke duk harkokin kula da ‘yan-gudun hijirar, wanda aganin shi hakan ne yake haddasar da rashin samun kwarewa.
Malam Bala Bello, wani mazauni arewacin Najeriya ne, da yake ganin akwai bukatar gwamnati, ta dauki kwararan matakai wajen ganin an inganta rayuwar mutane a sanssanin ‘yan-gudun hijirar, yana kuma ganin wadannan mutane ba kawai ‘yan abubuwan da ake basu ne kawai suke nema ba, suna bukatar fiye da haka.
Domin kuwa sukanji ance anfitar da makudan milliyoyi da billiyoyi don tallafawa ‘yan-gudun hijira, amma abun da kawai suke ganin ana ba mutane bai wuce, katifa, filo, robobi da dai makamantan su. Wanda idan har anfitar da wadannan makudan kudin, to mai ke sa ba suganin ana inganta rayuwar mutane? Don haka suna kara kira ga gwamnatoci da a nada kwamiti na amintatu don duba yadda ya kamata a gudanar da inganta rayuwar mutanen a duk sansanin 'yan-gudun hijirar.
Your browser doesn’t support HTML5