Akwai Bukatar Fita Kasashen Waje Domin Daukar Fim - Kannywood

Alhaji Alhassan Kwalli Jarumin Kannywood

A shirin mu na nishadi a yau mun samu bakwanci jarumi Alhassan A kwalli wanda ya shafe shekaru 29 yana harkar wasan kwaikwayo tun yana aji biyu a makarantar sakandare tun lokacin da ake wasan dandali daga nan ya koma wasan kwaikwayo a gidan talabijin kafin su fara home bidiyo sai gashi a yanzu suna kan satellite.

Alhaji Bushasha dai ya ce sha’awa ce ta kai shi ga harkar fim,sannan hanya ce da akan iya isar da sako wanda ke tasiri cikin alumma , ya ce harka ce da kan sama wa mutum arziki da suna da kuma daukaka.

Ko da ya ke ya ce kawo yanzu harkar fim ya samu cigaba ta hanyar amfani da kayayyaki zamani baya ga zuwa wasu kasahen domin daukar fim, sai dai ba dukkanin yan harkar fim ke samu damar fita kasashen wajen ba, suna bukatar kowanne dan wasa ya samu damar fita kasashen waje domin daukar fim ko samu damar yin bita a harkar fim din.

A fannin shegumi kuwa bayan shafe dogon hutu jarumi Ibrahim Mai Sinku ya dawo harkar fim inda ya fara da wani aikin da ake dauka a garin Kano mai suna 'Magajin Sarki’.