Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rayuwar Matasa Na Ta'allaka Kan Yanar Gizo


Yanar gizo
Yanar gizo

Kafafen sadarwa na yanar gizo, sun saukaka ma mutane rayuwa, babuma kamar matasa da ke mu’amala da wadannan abubuwan zamanin. Ta wadannan kafofin, mutun na iya ganawa da mutanen da bai san su ba, a fadin duniya cikin dakiku kadan.

Amma abun dubawa a nan shine, idan ba ayi hattara ba, da irin abubuwan da ake aikawa ba, a wadannan dakikun akan kaiga wasu mawuyatan halaye a rayuwa. Don haka da ace zamu yima kawunan mu adalci, kamin a dannan wannan botirin na aikawa, yana da kyau idan za'a sake duba abun da aka rubuta, don sake duba wasu abubuwa da basu kamata ace mutun ya rubuta ba, balle har ace ya aika ma duniya tagani.

A lokkuta da dama, yin hakan zai tai maka daga aika wasu abubuwa da kan samutun cikin kunya ko kuma wasu abu da zai iya batama wani rai. Wasu abubuwa da dama, da yakamata ace mutun ya guji sakawa a shafin yanar gizo, da suka hada da maganganu na kabilanci, bangaranci, rantsuwa, musu wanda ba zai haifar da abun alkhairi ba, kai harma da wasu hotuna da basu kamata ba.

A kuma guji daukan rubutun wani da yayi a shafin shi, batare da bayyanar da ai nihin asalin mai rubutun ba, "Wato satar basira" kuma muta ne su guji rubutun batanci ga shugabanni a wajen aikin su, da abokan aikin su a kan kowa ne irin hali. Haka kuma muta ne su guji rubutu a kan wata tafiya da za suyi don barin gari, wanda duk wadannan kan iya zama abun da zai haifar da munanan sakamako a karshe.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG