Dattin kunne na daya daga cikin abubuwan da basu da dadin gani, musamman ga yara da mata. Sau da yawa mutane su kanji ba dadi idan aka ga suna kwakular kunnen su, har ma idan suka fitar da datti.
Mafi yawan mutane kanyi amfani da audugar kanti wajen goge kunne, ko dai gare su ko ga yara. Bincike ya nuna cewar amfani da wannan audugar, na da lahani fiye da alfanun, domin kuwa tana iya hai far ma mutun da cutar, da mutun kan iya kurmancewa, babu kamar idan anyi amfani da ita ga yara.
A wasu shekarun baya a nan kasar Amurka, anyi wata yarinya da iyayen ta su ke mata amfani da wannan audugar, wajen goge mata kunne a kowane lokaci, wanda basu da masaniyar wannan audugar ta shiga cikin kunnen ta, har ta shafi dodon kunnen. A takaice da wannan yarinyar ta kasance bata jin magana, bayan wasu lokkuta. Hannah Horvath, ta bayyanar da cewar tun daga ranar da mahaifiyar ta, ta fara sa mata wannan audugar tafara samun damuwa da kunnen ta. Don haka ana kara jan hankalin mutane da su guji amfani da wannan audugar wajen goge kunne.