Yanzu haka dai wasu al'ummomi da ke fama da matsalar tsaro har sun gwammace da ma ace ba ‘yan Najeriya ba ne.
‘Yan Najeriya musamman na yankin arewa sun jima suna kokawa akan matsalolin rashin tsaro dake son ganin baya ga resu a sassa daban daban.
Al'ummomi a gabashin Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya sun jima cikin halin kunci akan ayukkan ‘yan bindiga kuma har yanzu ba wata mafita duk da koken da suke yi ga mahukunta.
Wannan ne ma ya sa harin da aka kaiwa ayarin shugaban Najeriya a jihar Katsina wasu ke ganin akwai abin ishara a ciki.
Aminu Almustapha Boza dan majalisar jiha ne wanda ya jima yana fafatuka akan matsalolin rashin tsaro a gabascin Sakkwato. Ya kuma ce maganar da yayi shekura biyar da suka wuce ya tabbata, ga shi yau an wayi gari ana tare ayarin gwamnoni da na shuwagabanin kasa.
Ku Duba Wannan Ma Yadda Jami'an Tsaro Suka Kubutar Da Mutum 77 Da Aka Tsare A Dakin Wata Mujami'a A Jihar OndoShi ma Gwamnan Aminu Waziri Tambuwal ganin ya ke yi akwai bukatar kara yiwa kasa addu'a da kuma fuskantar matsalolin da gaske.
“Abu ne da ke nuna akwai bukatar kara zage damtse ga yin addu'o'i, a kuma hada kai wuri daya a tunkari matsalar kuma dole a daina saka siyasa cikin sha'anin samar da tsaro, abu ne da ya shafi kowa ba wai shugaban kasa kadai ba ko kuma Muhammad Buhari zaman sa mutum ko Aminu Waziri Tambuwal a zaman gwamnan Sakkwato “
Duk kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Najeriya yayin rubuta wannan rahoton, akan hare haren da mazauna yankunan gabashin Sakkwato ke fuskanta ya ci tura.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5