Akawunan Kotu A Jamhuriyar Nijar Sun Shiga Yajin Aiki

NIGER: SHUGABA MUHAMMADOU ISSOUFOU

A Jamhuriyar Nijar yau akawunan kotu sun fara yajin aikin kwanaki biyu na gargadi da gwamanati, akan wasu tarin matsaloli da suka yi alkawarin magance musu a yayin zaman sulhu da su ka yi da gwamnati a shekara 2014.

Shuwagabannin kungiyar SNAJ ta akawunan kotu da ake kira Greffier sun kirawo taron manema labarai, inda suka nuna rashin jin dadin su, saboda mawuyacin halin da suke ciki, wanda ke da nasaba da rashin cika alkawarin da gwamnati ta dauka akan maganar inganta rayuwar masu aiki a kotuna.

Sakataran Kungiyar SNAJ, Malam Chaibou Kadade, ya ce, suna da matsaloli da dama wadanda suka mikawa gwamnati amma har yanzu sun kasa share musu hawayensu.

Sannan ya kuma ja hankalin gwamnati da ta gyara wata doka domin ma’aikata su samu ci gaba.

Daya daga cikin ma’aikatan mai suna Maitre Maina Zango ya ce, kusan makonni uku kenan da wannan kungiya ta aikawa da hukumomin shari’a wasika domin su sanar da su halin da ake ciki.

Ya kuma kara da cewa, sai dai har yanzu babu wata amsa mai gamsarwa da suka samu, dalilin da ya sa suka yanke shawarar shiga yajin aiki a ranakun 30 da 31 ga watan Janairu nan.

A kokarin da Sashen Hausa na Muryar Amurka ya yi domin jin bakin gwamnatin hakan bai samu ba.

Saurari cikakken rahoton Sule Mumuni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Akawunan Kotu A Jamhuriyar Nijar Sun Shiga Yajin Aiki