Williams, mai shekaru 104, ya rasu ne a cikin barcinsa da sanyin safiyar yau Litinin, 11 ga watan Satumba.
WASHINGTON, D. C. - An fi sanin Williams ne da Doyen mai sana’ar akawu a Najeriya, ya kuma taka rawar gani wajen bunkasa harkar hada-hadar kudi ta kasar.
Williams ya karanci lissafin kudi a Jami'ar London kuma ya samu mukami na matsayin babban akawu wato Chartered Accountant a shekarar 1947.
Bayan komawarsa Najeriya a shekarar 1952, ya kafa kamfaninsa na lissafin kudi, Akintola Williams & Co., wanda a yanzu ake kira Deloitte & Touche.
Ya kasance Shugaban Cibiyar Chartered Accountants of Nigeria (ICAN) daga shekarar 1963 zuwa 1965 kuma yana daya daga cikin wadanda suka kafa ta.