Rahotanni da maneman labaru suka fitar na cewa akwai wasu al'uman wasu 'yan kasashen ketare na China na cikin wadanda suka rasa rayukansu.
Ko da yake, fadar jakadanci kasar China da ke Accra ta fadawa Muryar Amurka cewa, saboda yanayin gawarwakin, ba za ta iya tantace wannan ikrari ba sai in hukumar 'yan sanda ta fito da bayani a hukumance.
Wani saurayi da ya shaida hatsarin wanda ya bukaci da a sakaya sunansa ya yi karin bayani bisa abin da ya afku inda ya ce wata babbar mota mai dauke da duwatsu ne ta yi karo da wata karamar mota wacce ta shige cikin babbar motar, lamarin da ya sa motar ta kama da wuta.
Hatsurran mota nada cikin masifun da ke ci gaba da lakume rayukan jama'a tare da tattalin arziki na kasar abin da wasu al'umma dora alhaki bisa wasu direbobin da ke kazamin gudu tare da shan kayan maye.
Hukumar 'yan sanda ta sanar da cafke direban babbar motar tare da fara bincike domin a ajiye doka a mazauninta.
Tuni dai aka adana gawarwakin a mutuware.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5