Akalla mutane takwas ne suka mutu a jiya Talata, sannan wasu da dama suka jikkata, bayan da wani mutum ya tuka wata babbar motar da ya hayo ya bi ta kan mutane a wata hanya da aka kebe domin masu tuka kekuna a birnin New York da ke nan Amurka.
A cewar magajin garin Birnin na New York, Bill de Blasio, yayin wani taron manema labarai, “bisa ga bayanan da suka samu, hari ne na ta’addanci, kuma na raggwaye wanda aka kai da nufin cutar da fararen hula da basu ji ba, ba su gani ba.”
Gwamnan New York, Andrew Cuomo ya bayyana harin a matsayin wanda “wani mutum guda ne ya kai shi”, yana mai cewa babu wata alama da ta nuna cewa harin wani bangare ne na wani gagarumin hari da aka shirya kai wa.
Kwamishinan ‘yan sandan Birnin, James O’Neill, ya ce da misalin karfe 3:05 na yamma, wani mutum da ke tuka wata motar pickup da ya hayo, ya kutsa kai cikin hanyar da aka tanadawa masu tuka kekune, ya bi ta kansu hade da masu tafiya a gefen titi.
Motar ta pickup har ila yau ta bugi wata motar ‘yan makaranta, inda wasu manyan mutane biyu da yara kanana biyu suka ji ciwo.
Daga bisani ne kuma maharin ya fice daga cikin motar yana rike da bindigogi biyu, inda daga baya ‘yan sanda suka harbe shi a ciki aka kuma tsare shi, a cewar kwamishina O’Neill.
Rahotanni sun ce an yi wa maharin tiyata, ana kuma sa ran zai rayu.
Ga karin bayani daga firar da abokin aiki ya yi da Alhaji Lukman Abbas, wani mazaunin birnin New York
Your browser doesn’t support HTML5