Akalla Mutane 50 Da Dabbobi Da Yawa Sun Kone Kurmus A Jihar Neja

DRCONGO-ACCIDENT-VICTIMS

Kimanin Mutane hamsin da Dabbobi masu yawa ne suka kone kurmus a wani mummunan hadarin mota da ya auku a jihar Neja da yammacin ranar Lahadi.

Rahotanni daga yankin karamar hukumar Kacha a jihar Neja da ke Najeriya sun bayyana cewa wata babbar motar tankar dakon man fetur tayi hadari a kan hanyarta ta zuwa Arewacin Najeriya daga kudancin kasar, sannan wata tirela dauke da dabbobi da mutane da yawa ta auka wa tankin man motar, lamarin da ya haddasa tashin wuta.

Dabbobi sun mutu a hadarin moto a Neja

Hadarin da ya auku da yammacin ranar Lahadi 8 ga watan Satumba ya janyo mummunar barna, nan take dai aka fara kokarin yin jana'izar wadanda suka mutu.

Shugaban kungiyar direbobin tankokin mai a jihar Neja, Kwamred Faruku Kawo, ya ce rashin kyawun hanyar mota ne ya haddasa wannan mummunan hadari mai matukar tayar da hankali.

Hadarin mota a Zimbabwe

Shugaban karamar hukumar Kacha Hon. Dallame Abdullahi Chaku, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce suna cikin yanayi na tashin hankali.

Matsalar rashin kyawawan hanyoyin mota wata babbar matsala ce a Najeriya da ke janyo asarar rayukan jama’a da kuma dukiya ta miliyoyin Naira a kasar, lamarin da ke bukatar daukar mataki cikin hanzari.