A shirinmu na mata da sana'o'i a yau mun samu bakonci Malama Aisha Umar Muhammad Gombe, mai sana’ar sayar da kayyayakin mata da maza, wanda ta shafe sama da shekaru 20 tana wannan sana’ar, kuma ta ce ta fara wannan sana’ar ne da jarin naira dubu dari biyar a wancan lokaci.
Ta ce babban abinda ya ja hankalinta fara wannan sana’ar dai bai wuce duba da cewar ta taso ta tarar da mahaifiyarta tana wannan sana’ar, inda ta ke sayarwa mata kayayyaki wanda da haka ne har ta samu jarinta na kanta ta kuma fara sayar da kayayyaki.
Ta ce tana kai kayayyakin ta garuruwa kamar su Kaduna, Birnin Kebbi, Sokoto, Borno a lokacin da duniya ke kwance, Aisha ta ce takan zaga jihohin arewacin Najeriya domin bada kaya, ga maza ko mata.
Amma kamar ko wacce sana’a ta ce tun da ta fara wannan sana’ar, ta taba shiga wata babbar matsala da wani dan siyasa da suka saba cinikayya tun shekara 2006, inda ya karbi kayan fiye da naira miliyan bakwai ba’a biya ta ba wanda sai da aka shafe shekaru kafin ya biya ta.
Sai dai wannan babban kalubalen da ta shiga har sai da yasa ta sayar da wasu daga cikin kaddarorin ta, inda ta sake tada sabon jari domin yin wasu sabbin kayayyaki da ta koma kan kafafunta, ta kuma kama sana’ar ta gadan gadan.
Ta ce babban burinta dai a yanzu shine ta bude babban shagon sayar da kayayyaki wato “Boutique” a wasu daga cikin jihohin da take kai kayayyakinta.
Your browser doesn’t support HTML5