Mukaddashin sakataren hukumar Ahmed Maigari ya ce la’akari da cusa kwaya da a ka yi wa Zainba Aliyu a lokacin Umrah, ya sa kiran ya zama wajibi don Saudiyya kan yanke hukuncin kisa ga irin wannan laifin.
Ita kuma jami’ar kula da abincin alhazai, Hajiya Ramatu Jafar Isa, ta ce akwai abinci mai tsafta da za a rabawa alhazan, don haka su guji cin abinci marar inganci daga Takari.
Tuni tawagar farko ta jami’an hukumar alhazai ta sauka a Madina don shirin tarbar alhazan karkashin jagorancin Muhammd Gire.
Shugaban hukumar alhazan Barista Abdullahi Muktar, ya ce masaukan alhazan na nan daf da harami a anguwar da ke zagaye da Haramin.
Jigilar alhazan dai za ta fara daga jihar Katsina da Kaduna da kuma Lagos.
Domin Karin bayani saurari cikakken rahotan Saleh Shehu Ashaka.
Your browser doesn’t support HTML5