Shugaban Hukumar Alhazan Najeriya Barista Abdullahi Mukhtar Muhammaed ya ce, in an dubi yadda canjin dala zuwa Naira ya ke kimanin shekaru 10 da su ka wuce, an samu raguwar kudin aikin hajji ne ga alhazan Najeriya.
Barista Mukhtar, wanda ke zantawa da Muryar Amurka a Abuja, ya ce baya ga jakar alhazai, duk sauran lamuran aikin hajji da dala a ke biyansu kama daga tikitin jirgi zuwa masaukai.
Shugaban na hukumar hajjin (NAHCON a takaice) ya ce, lura da wani ragi da a ka samu da ya shafi lamarin sauya hanyoyin da za a yi jigilar alhazan a Saudiyya, ya sanya samun ragin kimanin Naira dubu 51 da ake tunanin ko za a maida wa dukkan alhazan da su ka kammala biya.
Daya daga cikin kwamandojin ‘yan agaji na hidimar alhazan, Salisu Muhammad Gombe, shi ma ya ce sun shirya da aikin hidima ga maniyyatan.
10 ga watan yuli ne za a fara jigilar alhazan, inda za a fara daga alhazan jahar Katsina; za kuma a kammala biyan kudin kujerar a ranar 15 ga wata yuli.
Saurari Rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya Cikin Sauti
Facebook Forum