To sai dai masu fashin baki a al'amuran yau da kullum na cewa abin da kamar wuya, domin ba alamun da ake gani kenan ba
A karon farko Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ahmed Lawan ya mayar da martani ga wadanda ke cewa Majalisar ta zama 'yar anshin Shata ga baren zartarwa. Inda ya bada misalai yana cewa, da Majalisar da bangaren zartarwa kowa ya san matsayin sa, kuma kowa ya san aikin da ke gaban sa.
Ahmed Lawan ya ce ana ce mana yan amshin shata ko kuma tambarin roba amma ina gani masu fadin haka basu fahimce mu ba ne.
Ina so a tuna cewa mu ne muke sa ido a ayyukan bangaren zartarwa, kuma muna da kyakyawar fahimta a tsakanin mu, anan ina nufin tsakanin mu a majalisar dattawa da ta wakilai da bangaren gwamnati, sai mun hada kai sanan mu yi wa 'yan kasa aiki.
Karin bayani akan: Ahmed Lawan, APC, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Duk da haka mukan yi musayan yawu tsakanin mu da bangaren zartarwa, idan kun tuna akwai lokacin da muka kai ruwa rana akan batun sayan motoci, da kuma batun sayan kayan sawa a gidajen mu, irin su kujeru da sauran su, da mu yan amshin shata ne ai da ba a yi zazzafar Mahawarar da ta faru ba.
A baya Ahmed Lawan ya jagoranci majalisar wajen sukan gwamnati akan batun tsaro akai akai, har dai aka kaiga sauya Shugabanin hukumomin tsaro da suka kwashi tsawon lokacin akan mukaman su.
To sai dai kwararre a fanin kimiyar tsaro ta kasa da kasa Dokta Yahuza Ahmed Getso ya ce wadannan kiraye kiraye ba su isa ba, domin kasa tana cikin halin ha'u'la'i har yanzu. Saboda haka ba sa yi aikin su yadda ya kamata, ba sa kishin yan kasan,ba su damu da kwanciyar hankalin wadada suka za6e su ba.
Shi ma Malami a Jami'ar Baze da ke Abuja, Forfesa Usman Mohammed ya ce abu ne mai wuya Majalisar kasa ta kalubalanci bangaren zartarwa a bisa hujjojin cewa bangaren zantarwa sun taka rawa wajen nada su, shi ya sa ba a ganin suna kalubalantar Gwamnati akan bukatun jama'a.
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya sha alwashin hadin kan majalisa da bangare zartarwa da zai kawo sauye sauye masu ma'ana wanda yan kasa za su gani a kasa kafin karshen wa'adin mulkin APC a shekara 2023.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5