Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Gwamnoni Suka Sauya Matsaya Dangane Da 'Yancin Cin Gashin Kai Ga Bangaren Ma’aikatan Majalisa Da Shari’a A Najeriya


Wani lokaci da gwamnoni Arewacin Najeriyasuka yi taro a Jihar Kaduna
Wani lokaci da gwamnoni Arewacin Najeriyasuka yi taro a Jihar Kaduna

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun sauya matsayarsu a kokarinsu na samo mafita mai dorewa kan yajin aikin gama-gari sakamakon fafutukar da kungiyar ma’aikatan kungiyoyin bangaren shari’a da majalisun jihohi na Najeriya ke yi na neman a aiwatar da ‘yancin cin gashin kansu.

Kamar yadda jaridar Thisday ta ruwaito, gwamnoni sun cimma matsayar biyan majalisu wani kaso na hakokkinsu na wata-wata wajen daukar nauyin ayyukansu.

Wata majiya dai ta bayyana cewa, gwamnonin sun bada wannan matsaya ta su ne biyo bayan rashin amincewar kakakin majalisun jihohin kasar 36 da bada wani kaso da gwamnonin suka cimma matsaya a kai cikin hakokkin su na wata-wata na naira miliyan 100 don daukar nauyin ayyukansu ga duk majalisun jihohin na tarayyar kasar 36.

A nasu martani na kin amincewa da matakin da gwamnonin Najeriya suka cimma na daukar nauyin duk ayyukansu na naira miliyan 100 a duk wata, kakakin jihohin kasar 36 sun jadada cewa, ba za su amince da kasa da naira miliyan 250 ba a duk wata.

Haka kuma, majiyar ta ce, gwamnonin ma sun yi watsi da bukatun da kungiyar ma’aikatan bangaren shari’a ta Najeriya wato JUSUN da takwararta na kungiyar ma’aikatan majalisa ta Najeriya wato PASAN suka gabatar na cewa, gwamnati ta rika biyan kudaddensu zuwa lalitar bangarorin gwamnatin biyu kai tsaye.

Matsayin da gwamnonin suka cimma wanda aka aiwa take da “mai tsauri” ne ya haifar da jinkiri wajen warware yajin aikin da ma’aikatan shari’a da na majalisar dokoki suka shiga a cikin jihohi 36 hade da babban birnin tarayya Abuja don matsa wa gwamnonin lamba wajen tabbatar da aiwatar da yancin cin gashin kai ga bangarorin gwamnatin biyu da suka hada da ma’akatan shari’a da ma’akatan majalisu.

Har illa yau, gwamnaonin sun amince da cewa, hukumar NJC mai kula da ayyukan shari’a a Najeriya ne za ta kula da kudaden na majalisun shari’a na jihohi don kula da manyan kotuna yayin da gwamnatocin jihohi za su dauki nauyin bayar da kudade ga kula da kotuna majistare da kotunan gargajiya.

XS
SM
MD
LG