Mataimakin shugaban kungiyar IATA na Nahiyar Afrika da Gabas ta Tsakiya Muhammed Al bakair, ya ce bukatar ci gaban Afrika a harakar jiragen sama zai bukaci ginshikai kwarara. A kan haka ne kuma ya yi kiran samun kawance mai karfi tsakanin mambobin kungiyar, ya kuma ambato wasu kalubale da masana’antar ke fuskanta.
Ya ce akwai shaidun da su ke tabbatar da akwai sauran gurabun habbaka cinikayyar ci gaban tattalin arziki a Afrika. Ya buga misali yana cewa zamu iya tabatar da samun ginshikai da fasahohin cudeni-in-cudeka a Afrika don tattara haraji da kudaden fito
Mataimakin shugaban kasar Ghana, Muhmudu Bawumia ya bayyana cewar kasar Ghana na bibiyan burin da ake dashi ne ta kyautata amfanin aikin jiragen sama, wannan ne abin da kuma ya sa gwamnati ta dukufa wurin samar da yanayin tattalin arziki da ya dace da kuduri na siyasa don ya shafi bege na wannan fage a matsayin ajandar duniya da nahiya da kuma kasa
Taron na kwana biyu da ya maida hankali kan aikin jiragen sama domin ci gaba nahiyar zai baiwa malarta damar musayar kwarewar su don ci gaban wannan fage da ke kawo wa kasashen yammaci da tsakiyar Afrika cigaban tatalin arziki.
Ga rahoton wakilinmu a birnin Accra, Ridwan Muktar Abbas:
Your browser doesn’t support HTML5