Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan adawa Na Son a Tsige Firai Minista Brigi Rafini


Birgi Rafini
Birgi Rafini

Jam'iyyun kawancen na adawa a Jamhuriyar Nijar sun gabatarwa majalisar dokokin kasa takardar bukatar tsige frai minista kasar Birgi Rafini.

Jami'yyun adawa a Jamhuriyar Nijar sun bukaci a tsige frai ministan kasar daga mukaminsa saboda zargin gwamnatinsa da gazawa wajen kaddama da ayyuka da dama da suka shafi tafiyar da kasar, da kuma kasawa wajen tsaren zabubbukan 2021.

Kimanin ‘yan majalisa 35 na bangaren adawa ne suka saka hannu akan takardar da suka shigar a gaban majalisar dokokin kasar, domin bukatar tsige Brigi rafini.

'Yan adawa sun kuma zargi gwamnatinsa da gazawa wajen shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar.

Masu rinjaye wadanda ke kallon wannan yunkuri a matsayin wata alamar da ke fayyace mizanin dimokradiya a Jamhuriyar Nijar cewa suke ga ‘yan hamayya da a zuba a gani.

Daga cikin kujeru 171 na wakilici a majalisar dokokin kasa ‘yan adawa na da kujeru 35 yayin da PNDS Tarayya da kawayenta ke da kujeru 136.

A ka’idance, nan da sa'o'i 48 ne ya kamata bangarori su tafka mahawara kafin daga bisani a yi kuria’r raba gardama kan wannan batu.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG