Afirka Ta Kudu: Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Oscar Pistorius

Oscar Pistorius

A halin da ake ciki hukumomin sun ce Pistorius na da wata dama a watan Agustan badi inda zai sake neman a sake shi da wuri.

Tsohon fitaccen dan wasan tseren kafa na masu nakasa Oscar Pistorius a Afirka ta kudu, zai ci gaba da zama a gidan yari bayan da wata kotu ta ki amincewa da bukatar da ya gabatar ta a sake shi da wuri.

Tun a shekarar 2016 aka yankewa Pistorius hukuncin zaman gidan yari bayan da aka same shi da laifin kashe budurwarsa Reeva Steenkamp.

Hukumomin kula da gidajen yarin kasar ta Afirka ta Kudu sun ce kotun kolin kasar ta aike musu da wasika wacce ta nuna cewa zaman gidan yarin da Pistorius ya yi, bai kai iya wa’adin da za a sake shi ba.

A halin da ake ciki hukumomin sun ce Pistorius na da wata dama a watan Agustan badi inda zai sake neman a sake shi da wuri.

A Afirka ta kudu, fursoni na da damar a ske su da wuri idan har sun yi rabin wa’adin zamansu a gidan yari.