Hukumomin Afgahnistan sun ce wani dan kunar bakin wake ya ta da wata damarar bam da ke jikinsa, a wani shingen bincike da ke kusa da wata makarantar sakandire a tsakiyar birnin Kabul.
Harin ya faru ne da tsakiyar ranar yau Litinin, a kusa da wani wuri da aka kammala wata zanga zanga da aka kwashe kasa da sa’a guda ana gudanar da ita.
Akalla mutum shida suka mutu, ciki har da mata uku da kuma wasu jami’an soji biyu, sannan wasu mutane 20 sun ji raunuka.
Tun da farko, daruruwan mutane sun hallara a yankin domin yin zanga zanga, kan yadda harkar tsaro ke tabarbarewa a wasu Larduna biyu da suka hada da Ghazni da Uruzgan da ke kasar ta Afghanistan.
Matsalar tsaron ta fi tabarbarewa ne a wata guduma mai dauke da tsirarun mabiya mazhabar Shi’ar na bangaren da ake kira Hazara.
Masu zanga zangar sun watse ne bayan da shugaba Ashraf Ghani ya yi musu magana ta wayar tarho, inda ya tabbatar musu da cewa za a turo karin dakaru a yankunan domin tabbatar da tsaron.