Yawan cin hanci da rashawa a Afghanistan yana kawo koma baya ga kokarin da Amurka ke yi na sake gina kasar, a cewar wani rahoto da aka fitar a jiya Laraba.
WASHINGTON, DC —
Babban wakilin musamman na gwamnatin Amurka mai lura da da aiyukkan sake tada komadar kasar ta Afghanistan John Sopko, yace mutanen kasar Afghanistan da yawa ke korafi game da akidar cin hanci da rashawa da tayi katutu a wajen kusoshin gwamnatin kasar, musamman wajen mundahana da kayan bada agajin da ake aikawa kasar, abin da yake taimakawa ‘yan tawaye.
Rahoton na Sopko yace har yau akwai matsalolin tsaro, da na daidaituwar siyasa da na ci gaba, don haka yayi kira ga Amurka da ta ba matakan yaki da rashawa muhimmanci.