Jami’an binciken tarayya ne suka bada sanarwar wannan tuhumar da ake wa tsohon shugaban a jiya Laraba, wacce suka ce tana da nasaba da wani binciken da aka gudanar a Kampanin man fetir ta kasar mai suna Petrobras.
An zargi tsohon shugaban da matarsa da wasu mutane da dama da cin moriyar kudin kashe mu raba na gyaran wasu gidaje nab akin teku da wani kampanin gine-gine mai alaka da Petrobras suka gina. Lula ya musunta wannan zargin yana cewa ba shi keda wannan kadarar ba.