Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Dagewa Kasar Myanmar Takunkumin Tattalin Arziki


Obama Suu Kyi
Obama Suu Kyi

Shugaba Barack Obama na Amurka ya bada sanarwan cewa Amurka ta shirya dage takunkumin tattalin arziki da aka kakabawa kasar Myanmar (ko Burma), biyo bayan wata tattaunawa a fadar White House da shugabar kasar Aung San Suu Kyi.

Bayan tattaunawar tasu a jiya Laraba, shugabnnin biyu sun yi hira da manema labarai a nan ofishin shugaban Amurka, inda shugaba Obama yace yanzu Amurka ta shirya fid da takunkumi da ta sawa tattalin arzikin Burma na wani lokaci mai tsawo.

Bayan jawaban nasu, wani dan jarida ya tambayi shugaban kan ko yaushe ne Amurka zata dage wannan takunkumin sai Obama yace nan bada dadewa ba.

Tuni dai Obama ya aikewa majalisar dokokin kasar tashi da wasika cewar gwamanti ta kudiri aniyar maido da amfanonin cinikayya ga mutanen kasar Myanmar da aka dakatar dasu sama da shekaru 20 da suka shude saboda take hakkokin bil adama.

A nata kalaman, shugaba Aung San Suu Kyi ta godewa mai masaukin nata musamman da yake shne shugaban Amurka na farko da ya kai ziyara a kasar Myanmar. Ta kuma godewa majalisar dokokin ta Amurka da ta tilastawa Myanmar ta fara mutunta hakkokin bil adama.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG